
An gudanar da bikin yaye ƴan banga 600 da gwamnatin jihar Katsina ta ɗauki nauyin horaswa.
Taron yaye ƴan bangar dai ya gudana ne a sansanin jami’an tsaro na NSCDC da ke birnin Katsina inda daman nan ne a ka ba su horon.
Da ya ke jawabi a wurin taron, Gwamnan jihar Katsina, Rt Hon Aminu Bello Masari, wanda Sakataren Gwamnatin jihar ta Katsina, Alhaji Muntari Lawal ya wakilta ya yabawa mutanen da su ka nuna sha’awar su ta shiga aikin bangar domin su taimakawa al’ummar su.
Haka zalika, Gwamnan ya kuma sha alwashin cigaba da mayar da hankali wajen tabbatar da tsaron al’ummar jihar ta hanyar bayar da dukkan gudummuwa da goyon bayan da za’a bukata.
Gwamnan ya kara da cewa yanzu haka gwamnatin ta ware Naira biliyan 1.5 domin gudanar da ayyukan da suka shafi tsaron al’ummar jihar.
Tun da fari, mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin tsaro, Malam Ibrahim Katsina ya jinjinawa jami’an rundunar ta NSCDC bisa horon da suka ba yan bangar wanda yace zai taimaka sosai wajen shawo kan matsalar da ta addabi jihar Katsina.
Haka zalika Ibrahim Katsina ya bayyana cewa daga yanzu kam ba bu sauran sassauci daga gwamnati da al’ummar jihar Katsina ga ƴan bindiga tunda dai sun zaɓi yin fito-na-fito da su.
Mai ba Gwamna shawarar ya kuma bayyana cewa kawo yanzu gwamnatin ta horar da yan bangar 1,100 daga cikin mutane 3,000 da gwamnatin ta yi niyyar horaswa idan aka hada da wadannan 600 da aka yaye yau.
A jawaban su daban-daban, shugabannin hukumomin tsaron da suka magantu a yayin taron sun yaba da yadda shirin horaswar ya gudana cikin dan karamin lokaci kuma aka samu abunda ake so.