
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na ganawa da gwamnonin jihohi 36 na ƙasar nan sakamakon halin matsin rayuwa a fadar shugaban shugaban ƙasa da ke Aso Rock, Abuja.
Ganawar dai ana ganin ba za ta wuce a kan halin hauhawar farashin da mastin raguwa da ake ciki, inda hakan ya haifar da fusata a wasu sassa na ƙasar.
Ko a jiya Laraba ma, masu rike da masarautun gargajiya na ya kin arewacin ƙasar nan sun yi taro, inda su ka nuna damuwa a kan tabarbarewar tattalin arziki da ke ci gaba da yin ƙamari .
Wannan shi ne karo na biyu da shugaban ke ganawa da gwamnonin jihohi tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.