
Mazauna yankin Bwari na babban birnin tarayya Abuja sun koka da rashin ruwan sha a yankunansu.
Mazauna yankin sun lura cewa abin mamaki ne a ce babbar hanyar samar da ruwan sha a babban birnin tarayya Abuja da kewaye, tana cikin yankinsu, amma ba su da ruwan sha.
“A wajensu, lamari ne na, “Ruwa, ruwa ko’ina, nan kuwa ba ko digon ruwan da za a sha”.
John Awoyi, shugaban kungiyar matasan Bwari, ya ce al’ummomin yankin da suka hada da Igu, Kawu, Gaba da Zuma, ba su da hanyar samun ruwan sha, sai dai ma sun dogara da ruwan sama da magudanan ruwa.
Ya ce, “Ko da yake wasu wuraren suna da rijiyoyin burtsatse, ko dai ba su da kyau ko kuma ba za su ishi al’ummar yankin ba.
“Hatta asibitocin mu ba su tsira daga wannan kalubale ba; yawancin Cibiyoyin Kula da Lafiya na Farko (PHCs) a cikin al’ummominmu ba su da ruwan sha.
“Muna bukatar kulawar gwamnati cikin gaggawa a dukkan matakai, ciki har da kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda za su iya ba da taimako.”