23.1 C
Abuja
Tuesday, February 7, 2023

Mbappe ya doke Messi da Ronaldo a jerin attajiran yan kwallon kafa na Forbes

Must read

 

 

Kylian Mbappe ya kasance a kan gaba a jerin ‘yan wasan kwallon kafa da su ka fi samun kudi a Forbes – karo na farko da wani da ba Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo ba ya zama na daya tsawon shekaru tara.

A cewar kididdigar Forbes, kamar yadda BBC ta ruwaito, dan wasan gaban na kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain Mbappe, mai shekara 23, zai samu dala miliyan 128 (£115.2m) a kakar wasa ta bana.

Abokin taka ledar Mbappe na PSG, Messi ne na biyu akan dala miliyan 120 (£108m) sai kuma dan wasan gaban Manchester United, Ronaldo na uku akan dala miliyan 100 (£90m).

Neymar da Mohamed Salah ne suka cika na biyar. Dan wasan gaba na PSG da Brazil, Neymar zai samu kimanin dala miliyan 87 (£78.4m) a shekarar 2022-23 da kuma dan wasan gaba na Liverpool Salah $53m (£47.7m). Dan wasa na karshe da ya hau jerin sunayen banda Ronaldo ko Messi shi ne tsohon kyaftin din Ingila David Beckham a shekara ta 2013.

Mbappe ya rattaba hannu kan sabuwar kwangilar shekaru uku mai tsoka da PSG a watan Mayu, wanda ya kawo karshen rade-radin sauya sheka zuwa Real Madrid a bazara. Dan wasan, wanda ya lashe gasar cin kofin duniya ta Faransa, ya dauki kofina 11 a kungiyar, ciki har da gasar Ligue 1 guda hudu, tun bayan komawarsa daga Monaco da farko a matsayin aro a 2017.

Erling Haaland, wanda ya ci wa Manchester City kwallaye 19 a wasanni 12 tun bayan komawarsa a kakar bana daga Borussia Dortmund , ya shiga cikin jerin manyan yan kwallon kafa 10, Inda ya ke a lamba 6.

Dan wasan na Norway yana daya daga cikin ‘yan wasan Premier hudu a cikin 10 na farko tare da Ronaldo, Salah da kuma abokin wasan Manchester City Kevin de Bruyne. Haaland da Mbappe ne kawai ‘yan wasa a cikin jerin ‘yan kasa da shekaru 30.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article

- Website Designed By DEBORIAN.COM, a Nigerian Web Designer and Web Developer -