Home Labarai Miloniyoyi 300 ne za su tsere daga Najeriya a 2024 – Rahoto

Miloniyoyi 300 ne za su tsere daga Najeriya a 2024 – Rahoto

0
Miloniyoyi 300 ne za su tsere daga Najeriya a 2024 – Rahoto

An yi hasashen Najeriya za ta yi asarar miloniyoyi har guda 300 zuwa wasu kasashe a 2024, a cewar wani rahoto akan hijira daga Kamfanin Henley & Partners.

A cewar rahoton, kusan miloniyoyi 128,000 na duniya ana hasashen za su yi ƙaura zuwa wasu ƙasashe a 2024 da muke ciki, inda Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE, da Amurka ke kan gaba a jerin wuraren da za su je.

Rahoton ya bayyana cewa hijirar miloniyoyi ita ce kan gaba wajen nuna lafiyar kasa da tattalin arzikinta.

Henley & Partners kamfanin ne na Biritaniya wanda ke gudanar da ayyukan ba da shawarwari ga gwamnatoci na duniya akan gudun hijira da saka hannun jari.

Rahoton ya bayyana Najeriya a matsayin ta tara daga cikin manyan kasashe 10 da ake hasashen za su yi asarar dimbin attajirai zuwa wasu kasashe.