MOURINHO ZAIYI ZAMAN SULHU DA POGBA DA LUKE SHAW

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Rahotanni daga qasar ingila sun bayyana cewa mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Manchester United, Jose Mourinho zai tattauna da yan wasan qungiyar guda biyu da baya shiri dasu wato Paul Pogba da Luke Shaw.

Mourinho dai baya shiri da Pogba sosai inda takai ma basa Magana sosai kuma ya ajiye xan wasan a wasan da qungiyar ta buga na qarshe na wasan cin kofin qalubale na FA  da qungiyar Brighton Albion a sati biyun da suka  gabata.

Shima Shaw an bayyana cewa basa ga miciji da Mourinho bayan da Mourinho yafito fili ya soki xan wasan bayan an tashi daga wasan da qungiyar ta buga na gasar cin kofin FA kuma a lokuta da dama daman Mourinho yakan soki xan wasan.

Mourinho dai ya shirya tattaunawa da waxannan yan wasa ne domin kawo kwanciyar hankali a qungiyar sannan kuma domin ganin qungiyar taci gaba da samun nasara a wasanninta batare da ansamu rabuwar kai acikin yan wasan qungiyar ba.

Tattaunawar dai zata gudana ne domin a fahimci juna sannan kuma kowa yafaxi abinda yake faruwa daga baya kuma asamu yadda za’ayi a kawo gyara da kuma gujewar faruwar abin anan gaba.

Manchester United dai zata fafata da qungiyar Swansea City a yau Asabar da misalin qarfe uku na rana yayinda kuma qungiyar take matsayi na biyu da maki 65 akan tebur sai kuma Swansea take mataki na 14 da maki 31.