
Manyan kamfanonin sadarwa guda hudu da ke aiki a Najeriya sun fara wani yunkuri da za su kara farashin kiran waya a kasar.
Kamfanonin da suka hada da Glo da MTN da Airtel da kuma 9Mobile suna rokon gwamnatin tarayya da ta kawo sauki mai ma’ana a masana’antar.
A cewar kamfanonin, yanayin tsarin kula farashi a halin yanzu bai yi daidai da yanayin tattalin arziki da ake ciki ba, don haka suke neman taimakon gwamnati don magance kalubalen farashin.
Kamfanonin sadarwar guda hudu sun ce su kadai ne ba su yi karin farashi ba, wanda aika ce hakan na barazana ga dorewar masana’antar da kuma yiyuwar kashe gwiwar masu zuba jari.
Sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyar dillalan sadarwa ta Najeriya, ALTON, da kungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya (ATCON) suka fitar a yau Alhamis.
A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban ALTON, Mista Gbenga Adebayo, da shugaban ATCON, Mista Tony Emokpere, kamfanonin basu yi ƙarin farashi ba cikin shekaru 11 da suka gabata.
Sun danganta rashin karuwar ga matsalolin da suka shafi ka’idoji duk da mawuyacin halin tattalin arziki.