Robert Mugabe

Jami’an tsaron soji na kasar Zambabwe sun karbe ikon babbar birnin kasar Zambabwe daga hannun ‘yan sandan kasar a ranar larabar nan, abinda yake ishara zuwa ga juyin mulki ga shugaban kasar Robert Mugabe da shafe kusan shekaru 40 yana jan ragamar kasar.

Gidan talabijin na kasar Zambabwe ya ruwaito sojojin kasar na bayanai kan cewar, sojan kasar sun karbe ikon ne da babban birnin kasar Harare. Jami’an tsaron sun girke manyan motocin sulke a titinan biranen kasar.

“Muna masu sanar da al’umma cewar, mai girma shugaban kasa tare da iyalinsa, suna kulawa ta musamman, kuma ana basu kulawar tsaro ta musamman” Manjo Janar Sibusiso Moyo ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a gidan talabijin din kasar.

“Muna fuskantar kalubalen tsageru, domin fuskantarsu da dukkan kalubalen da suka zo da shi, daga zarar mun kammala wannan aiki na dakiles u, kuma komai ya koma yadda yake a baya, ba zamu mayar da hannun agogo baya ba”

Wadannan kalamai dai na kara nuna kalubalen da Mugabe dan shekaru 93 yake fuskanta na komawa kan karagar mulkinsa, wanda yake mulkin kasar tun shekarar 1980, bayan samun ‘yancin kasar daga hannun Birtaniya.

Jam’iyyar dake mulkin kasar ZANU-PF a ranar talatar da ta gabata, ta zargi babban hafsan tsaron kasar Janar Constantino Chiwenga da kalaman rashin da’a ga shugaba Mugabe sabida ya cire mataimakin shugaban kasar Emmerson Mnangagwa.

Bayan cire Mnangagwa daga mukamin mataimakin shugaban kasa, hakan ya share hanya ga uwargidan shugaba Mugabe, Madam  Grace ‘yar shekaru 52 domin zama mataimakiyar shugaban kasa, wadda ake ganin zata gaji mijinta Mugabe a matsayin shugabar kasar Zambabwe ta gaba, abinda jamian tsaron kasar suka ce ba zata sabu ba.

A lokacin da alamura suka tsananta a daren jiya, an jiyo karar harbe harben bundiga a daura da masaukin shugaba Mugabe na musamman.

Tuni dai ofishin jakadancin Amurka ya gargadi ‘yan Amurka mazauna kasar da su kauracewa duk wani abu da ya shafi siyasar kasar,  duba da yadda aka shiga halin rudani a kasar.

Ana ta jiya amo da amsakuwwar motocin jami’an tsaro a sassa da dama na babban birnin kasar harare.

Har ya zuwa wannan lokaci manyan jami’an Gwamnatin shugaba Mugabe babu wanda ya yi magana kan abinda ke faruwa, wanda hakan ke kara tabbatar da cewar jami’an tsaron sojin kasar sun ci lagwan gwamnatin Mugabe.

Ana dai kyautata zaton lamarin zai juye zuwa juyin muki nan da wani dan lokaci kankani.