
Kungiyar Dattawan Arewa, NEF, ta bayyana nadamar ta ta goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaben 2023.
Da yake magana yayin tattaunawa da jaridar Guardian, kakakin NEF, AbdulAziz Suleiman, ya ce kuskuren zaben Tinubu ya koya wa yankin darasi mai ɗaci.
Sai dai ya ce a ci gaba, Arewa za ta ba da fifikon hadin kai da fahimtar juna wajen zaben shugaban ƙasa.
Suleiman ya ce: “Arewa ta yi kuskure wajen zaben Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2023, kuma da wuya su sake maimaita kuskuren nan gaba.
“Sun koyi darasi daga kura-kuran da suka yi a baya kuma za su yi kokarin zabo dan takarar da zai iya hada kan kasar nan tare da gudanar da mulki domin amfanin ‘yan Najeriya baki daya.
“A nan gaba, Arewa za ta yi taka-tsan-tsan wajen zabar dan takarar shugaban kasa,” in ji shi