Home Labarai Muna bakin cikin yin bikin Kirsimeti ba tare da mun karɓi albashi ba — Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Muna bakin cikin yin bikin Kirsimeti ba tare da mun karɓi albashi ba — Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

0
Muna bakin cikin yin bikin Kirsimeti ba tare da mun karɓi albashi ba — Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Ma’aikatan gwamnatin tarayya a fadin kasar nan na kokawa kan jinkirin biyan albashin watan Disambar 2023.

Sun ce abin bakin ciki ne da suka yi bikin Kirsimeti a jiya ba tare da albashinsu ba, lamarin da ya shafi iyalansu, musamman wadanda ba su da ajiyaiyun kuɗaɗe.

Da yawa daga cikin wadanda suka zanta da Daily Trust sun koka kan yadda ba su yi bikin Kirsimati cikin wadata ba kamar yadda al’adar take ta yin girke-girke, da sanya sabbin tufafi da kuma kai ziyarce-ziyarce.

Binciken da Daily Trust ta yi ya nuna cewa dukkan ma’aikatan da ke ma’aikatun gwamnatin tarayya, wasu na ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya (OHoCSF), da kuma wasu da ke ofishin sakataren gwamnatin tarayya (OSGF) sun ce lamarin ya kasance ba zato ba tsammani.

An gano cewa lamarin haka yake a jami’o’in gwamnatin tarayya da makarantun gaba da Sakandire na tarayya, da kwalejojin ilimi da sauran cibiyoyin gwamnatin tarayya a duk fadin kasar nan.

Majiyoyi sun ce ma’aikatan hukumomin samar da kudaden shiga kamar NNPC, NPA, NIMASA, NCC, CBN, FIRS, da dai sauransu ne kawai suka albashin watan Disamba.