Shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC Ibrahim Magu ya bayyana cewar suna buncikar bidiyon Ganduje a Landan.

Shugaban hukumar ya bayyana haka ne a lokacin da wani dan fafutikar Yaki da cin hanci da rashawa Bulama Bukarti yayi masa tambaya lokacin da aka yi wata ganawa tsakanin Shugaban hukumar EFCC da ‘yan Najeriya mazauna kasar Burtaniya.

Magu ya bayyana cewar yanzu haka sun baiwa kwararru dama domin yin binciken kwakwaf akan wannan faifan bidiyo da aka nuno Gwamnan Kano Ganduje na sanya daloli a cikin babbar riga.