Categories
Labarai

Mutane 15,897 suka ci jarrabawar daukar Malaman makaranta a Kaduna

 

Hassan Y.A. Malik

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa mutane 15,897 ne suka samu nasarar tsallake jarabawa ta farko da ta biyu da gwamnatin jihar ta yi don daukar malaman firamare masu inganci don su mayae gurbin wadancan da aka kora.

Gwamnan ya bayyana hakan ne jiya bayan ya fito daga wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin ciyar da jihar Kaduna gaba, inda a nan ne suka tattauna yadda yanki na karshe na daukar malaman zai kasance.

El-rufa’i ya ce, akwai wani rahoto da ya iske shi na cewa wasu bata gari sun jefa sunayen wasu mutane da ba su ci jarrabawar ba.

“hakkinku ne ku tsamo wadancan mutane, ta yadda ba za mu yi kitso da kwarkwata ba,’ El-Rufa’i ya ce ga kwamitin tantancewar.

Ya kuma yi kira ga kwamitin tantancewar da su ji tsoron Allah su gabatar da aikinsu ba tare da ha’inci ba ta hanyar nuna kabilanci ko addini ko ma karbar na goro.

“Ku yi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa ku daukar mana malaman firamare da za mu yi alfahari da su a nan gaba.”

Ja’afaru Sani, the state Commissioner for Education, Science and Technology, noted that the screening was rigorous.

Kwamishinan ilimi na jihar Kaduna, Ja’afaru Sani, ya bayyana cewa tantancewar malaman na da matukar wahala kasancewar umarni da gwamna ya bayar na a tabbata an dauki mafi hazaka daga cikin dimbin mutanen da suka zana jarrabawar.

Shugaban hukumar ilimin bai daya matakin farko na jihar, Nasir Umar, ya ce za a lika sunayen wadanda suka yi nasara a sakateriyar kananan hukumominsu, kuma an nada mutune uku a kowace karamar hukuma 23 da ke jihar don tattance wadanda suka yi nasarar.

Za a dauki tsawon kwanaki 10 ana tantancewar, kuma za a fara daga ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu, 2018, inda a kowace rana aka bukaci kwamitin da ya tantance mutum 70 a kowace karamar hukuma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *