
Akalla mutane 145 aka ce an kashe a harin da ‘yan bindiga suka kai kauyuka 23 a jihar Plateau.
Rahotanni sun ce maharan sun kashe mutane 113 a kauyuka 20 da ke karamar hukumar Bokkos da kuma 32 a kauyuka uku da ke karamar hukumar Barkin Ladi.
Daily Trust ta tattaro cewa an kai harin ne a kauyukan tun daga daren ranar Asabar zuwa safiyar ranar Litinin.
An kuma ce hare-haren sun yi sanadin jikkata daruruwan mutane tare da lalata dukiyoyi.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Ruku, Hurum, Darwat, Mai Yanga Sabo da kuma NTV dake cikin gundumomin Gashish da Ropp.
Shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Bokkos, Monday Kassah, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a jiya.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred domin jin ta bakinsa, bai amsa sakon kar-ta-kwana da wakilin Daily Trust ya aika masa ba.
Kassah, ya shaidawa manema labarai a jiya Litinin cewa an gano gawarwaki 113 daga hare-haren.
“Hare-haren sun kasance cikin shiri sosai, a kalla ƙauyuka daban-daban har 20 ne ‘yan bindigar suka kai hari a kai,”