Home Labarai Mutane shida sun mutu a rikici tsakanin ƴan bindiga da ƴan banga a Sakkwato

Mutane shida sun mutu a rikici tsakanin ƴan bindiga da ƴan banga a Sakkwato

0
Mutane shida sun mutu a rikici tsakanin ƴan bindiga da ƴan banga a Sakkwato

Wani rikici da ya auku tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan banga a garin Gada na jihar Sakkwato ya yi sanadin mutuwar mutum akalla shida, ciki har da wasu kwamandandojin ‘yan banga biyu.

Wannan lamari ya faru ne yayin da matsalar hare-haren ‘yan bindigan ke ci gaba da addabar jama’ar yankin na Gada.

Wani mazaunin garin ya bayyanawa BBC cewar: ”Ranar Alhamis da ‘yan bindigar suka kaiwa wani kwamandan ‘yan banga farmaki inda suka kashe shi nan take, ranar Juma’a kuma suka tare wani kwamandan a hanya tare da ‘kaninsa suka kashe shi bayan sun sassara ‘dan’uwansa da adda.

Duk da ya ke ‘kura ta lafa mutumin mazaunin garin na Gada ya bayyana cewar, sun jima suna fama da hare-haraen ‘yan bindida. ” Tsawon shekaru uku, idan maraice ya yi sai magidanta su fita wajen gari ‘dauke da fitilu da makamai suna gadi ya yinda a wasu garuruwan da maraice ta yi wasu ko sallar Isha’i ba sa iya samun yi zasu fita wajen gari kuma ba zasu dawo ba sai da asuba, idan ka ga an bar mutum cikin gari, to tsoho ne amma duk wani mai jin ‘karfi ko mace ko namiji ko yara zasu tsere daji su ‘buya su kwanta ba zasu koma gida ba sai da asuba. A wasu yankunan ko noma ba a yi isan gonaki sun yi nisa da gari saboda ko da ‘yan bindigar basu ‘dauke mutum to suna yi masa duka”.

BBC Hausa