Home Labarai Mutane 48 sun kamu da cutar ƙyandar biri a cikin kwanaki 6 – NCDC

Mutane 48 sun kamu da cutar ƙyandar biri a cikin kwanaki 6 – NCDC

0
Mutane 48 sun kamu da cutar ƙyandar biri a cikin kwanaki 6 – NCDC

 

 

An samu ƙarin mutane 48 sun kamu da cutar ƙyandar biri daga 8 ga zuwa 14 ga watan Agusta.

An samu ɓullar cutar a jikin mutane 48 a jihohi 16, kamar yadda Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya, NCDC ta bayyana a shafinta na yanar gizo a jiya Asabar.

NCDC ta bayyana cewa jihar Legas ce ke kan gaba a jerin sabbin masu kamuwa da cutar da mutum 15, yayin da Abia da Ogun suka samu mutum 5 kowanne.

Benue, Edo, Rivers da kuma FCT sun sami mutane 3 kowanne; Bayelsa da Ondo suna da guda biyu kowanne, yayin da Cross River, Anambra, Gombe, Imo, Katsina, Oyo da Osun suka samu guda ɗaya kowannen su.

Sabbin waɗanda su ka kamu da cutar sun ƙara adadin waɗanda suka kamu da cutar a Nijeriya tun daga farkon shekara zuwa 220, in ji NCDC, inda ta kara da cewa an samu bullar cutar a jihohi 29.

Ta kuma bayyana cewa daga cikin mutane 220 da suka kamu da cutar, maza sun kai 144, yayin da 76 kuma mata ne.

Ta ƙara da cewa kawo yanzu an samu rahoton cewa mutane 4 ne su ka mutu sakamakon cutar a jihohi hudu – Delta, Legas, Ondo da Akwa Ibom.

Cutar ta ƙyandar biri ta kashe jimillar mutane 12 a Najeriya tun watan Satumban 2017, in ji NCDC.