Home Labarai Mutane 4 sun tsira yayin da gini mai hawa huɗu ya ruguje a Abuja

Mutane 4 sun tsira yayin da gini mai hawa huɗu ya ruguje a Abuja

0
Mutane 4 sun tsira yayin da gini mai hawa huɗu ya ruguje a Abuja

Wani gini mai hawa hudu ya ruguje a Unguwar Garki da ke Abuja, inda wasu suka makale a cikin ɓaraguzai.

Shaidun gani da ido sun ce ginin bene mai hawa hudu da ke otal din Westbrook, a unguwar Garki 11, ya ruguje ne da misalin karfe 8:32 na daren jiya Litinin, bayan da leburorin da ke aiki a wajen suka tashi daga aiki.

Wani mazaunin Garki, Joseph Habila, ya ce rugujewar ginin ta haifar da tsoro da fargaba a tsakanin mazauna yankin sakamakon karar rushewar.

“A gaskiya Allah ne kawai Ya tseratar da ni saboda na je wani shago da ke kusa da ginin na yi siyayya ‘yan mintoci kadan na bar wajen, a lokacin da ginin ya ruguje,” inji shi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuj, SP Adeh Josephine, ta fitar a yau Talata, ta ce ƴansanda sun samu kiran waya da misalin karfe 8:40 na dare cewa ginin ya ruguje.

Adeh ta kuma ce an sanar da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da hukumar kula da gine-gine ta babban birnin tarayya Abuja akan lamarin.

Ta ce nan gaba za a sanar da al’umma karin bayani a kan lamarin.

Daily Trust