Home Labarai Mutum 10 sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a jihar Katsina

Mutum 10 sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a jihar Katsina

0
Mutum 10 sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a jihar Katsina

Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ya bayyana cewar akalla mutum goma ne suka rigamu gidan gaskiya a rikicin manoma da makiyaya da ya kaure a yankin karamar hukumar Safana.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da wata kungiyar fafutikar kare mata da kananan Yara ta kai masa ziyara a fadarsa a ranar Laraba.

“Mun samu rahoto a ranar Lahadi wasu bakin Fulani sun yiwa karamar hukumar Safana tsinke, inda suka farwa gonakin mutane suka cinye su sannan suka kashe mutum goma a cikin manoma”

“Sarkin ya Kara da cewar wannan abinda ya faru sharrin kwaya ne, yadda za a ce Yaro kankani ya kashe mace sa’ar mahaifiyarsa kuma ya yiwa gawar fyade “ Idan ba kwaya ba ba abinda zai sanya mutum haka.