
Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun kai hari kan ayarin motocin sharar-fage na Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari a jihar Katsina.
Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya tabbatar da harin a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata.
Ya ce an kai wa ayarin motocin sharar-fagge na jami’an tsaro hari, jami’an tsare-tsare da kuma masu yaɗa labarai gabanin tafiyar shugaban kasa zuwa Daura domin yin Sallah a kusa da Dutsinma a Katsina.
Maharan, a cewar Shehu, sun buɗe wa ayarin motocin wuta ne daga inda suka yi musu kwanton ɓauna, amma jami’an soji, da ‘yan sanda, da hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, tare da ayarin motocin suka maida martani har su ka samu nasarar fatattakar su.
“Fadar shugaban kasa ta bayyana a matsayin abin bakin ciki da rashin jin dadi, lamarin harin da ya faru a kusa da Dutsinma, jihar Katsina, a kan ayarin motocin da ke dauke da jami’an tsaro na sharar-fage tare da kuma jami’an tsare-tsare da na yada labarai gabanin tafiyar shugaban kasa, Muhammadu Buhari zuwa Daura domin yin Sallah.
“Maharan sun bude wa ayarin motocin wuta ne daga inda suka yi musu kwanton bauna amma sojoji da ‘yan sanda da jami’an DSS da ke tare da ayarin sun dakile harin.
“Mutane biyu da ke cikin ayarin motocin sun ji raunuka kuma su na karbar magani kan kananan raunukan da suka samu. Duk sauran ma’aikata, ma’aikata da ababan hawa sun isa Daura lafiya,” in ji Shehu.