Home Labarai NAFDAC ta kama magungunan ma’aurata na sama da Naira Miliyan 12 a Sokoto

NAFDAC ta kama magungunan ma’aurata na sama da Naira Miliyan 12 a Sokoto

0
NAFDAC ta kama magungunan ma’aurata na sama da Naira Miliyan 12 a Sokoto

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC, ta kama kwakayen magungunan jima’i da kudinsu ya kai Naira miliyan 12 a Sokoto.

Ko’odinetan hukumar ta NAFDAC a jihar, Garba Adamu, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, a yau Litinin cewa, tawagar da ke sintiri na hukumar ta yi nasarar kama su ne a yayin gudanar da aikin sintiri da suke yi na yau da kullum a kasuwannin jihar da kewaye.

Malam Adamu ya bayyana cewa kayayyakin ba su da rijista, kuma ba su da inganci sosai, inda ya kara da cewa “su na da haɗari ga lafiyar al’umma baya ga yadda ake amfani da hotunan batsa wajen tallansu.”

Ya kuma yi kira ga jama’a da su daina siyan irin wadannan kayayyaki daga wuraren da ba su da lasisi, inda ga kuma yi kira ga mutane su guji amfani da irinsu dan kau cewa kamuwa da cututtuka.

Ya kuma bukaci ƴan Najeriya da su rika duba matakan rajistar hukumar ta NAFDAC da kuma kwanakin karewar amfanin kayayyakin kafin amfani da su.