Home Labarai Najeriya ba talakar ƙasa ba ce, in ji mai-ɗakin Tinubu

Najeriya ba talakar ƙasa ba ce, in ji mai-ɗakin Tinubu

0
Najeriya ba talakar ƙasa ba ce, in ji mai-ɗakin Tinubu

Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce Najeriya ba talakar ƙasa ba ce, inda ta yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaki talakawa.

A cikin sakonta na Kirsimeti bayan gudanar da bikin Kirsimeti ga yaran gidan marayu na Nana Berry a Abuja a yau Asabar, Remi ta ce 2024 za ta zama alheri ga ƴan Najeriya, yayin da ta shawarci iyaye da su ci gaba da ƙarfafa wa ƴaƴansu gwiwa.

Ta ce, “Yayin da muke shiga shekarar 2024, ya kamata saƙonmu ya zama yadda za mu canza rayuwar matasa. Ko wane ne mu, mu daina maganar talauci a gaban ‘ya’yanmu, mu ba talakawa ba ne, masu hannu da shuni su ma su kula da talakawa su yi masu arziki, abin da ake bukata kenan.

“Mun cire batun talauci daga wannan mahallin domin hakan na gurbata zukatan matasa, amma dole ne mu ƙarfafa musu gwiwa tare da nuna musu rayuwa mai inganci.

“Za mu shiga shekara mai cike da alheri kuma wadanda suka yi imani da cewa za ta zama alherin su za su ji dadin ta”