
Farfesa Abubakar Adamu Gwarzo ya bayyana kwarin guiwar sa na cewa ƴan Najeriya da dama a nan gaba za su daina tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare domin samun ingantaccen ilimi.
Dan kasuwa kuma wanda ya kafa jami’ar Canada ta Najeriya da ke Abuja ya yi wannan tsokaci a lokacin da ya ziyarci makarantar.
Gwarzo ya yi nuni da cewa, da karuwar jami’o’i masu zaman kansu a fadin kasar, yawancin ‘yan kasar za su gwammace su yi karatu a gida nan da shekaru kamar ashirin.
Ya ce kishin bunkasa ilimi mai inganci ya sa shi ya kafa jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria da Franco-British International University da ke Kaduna.
“Mun tabbatar da hakan a Kano tare da kafa Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria, tare da ingantattun tsare-tsare, ingantattun malamai da kuma cancanta.
“Duba yawan ingantattun jami’o’i masu zaman kansu, za ku yarda da ni cewa makomar ilimi tana da haske sosai. A cikin shekaru 20, yawancin ‘yan Najeriya ba za su je wasu kasashe don neman ilimi mai inganci ba, a gida za su samu ilimin da suke nema,” in ji shi.