Zaman kare a karofi

Daga Yasir Ramadan Gwale

Rashin tsari da bin ka’ida na daya daga cikin dumbin matsalolin da suka dame mu. Idan za’a yi bayani na gaskiya kan irin dumbin matsalolin da suke dabaibaye da wannan al’umma tamu ta Nigeria, bai wuce irin zaman rashin tsari da rashin son kowace irin ka’aida ba, a harkokin rayuwa na yau da kullum, a koda yaushe, da yawan mutane sun fi son gudanar da al’amuran rayuwarsu, cikin rashin bin tsari da kiyaye ka’ida. Ana rayuwa tamkar zaman kare a karofi.

Yana daga cikin ayyukan hukuma na wajibi, tilasta mutane bin ka’aida, da shiryawa mutane bin tsarin da ya dace da hankali da addini da kuma al’ada. Wannan shi ne ke bayuwa zuwa ga samarwa da al’umma tarbiyya. Domin ita tarbiyya, ana dora mutune akanta ne, domin saita musu rayuwa ta dace da yadda ya kamata a gudanar da ita, kuma ta dace da hankali da yanayin rayuwar mutane.

Wajibin hukuma ne ta sanyawa mutane bin tsari. Amma sau da yawa abinda yake faruwa shi ne akasi, mutane daman bisa dabi’arsu basa son bin tsari da ka’ida. Misali idan muka dauki harkar sufuri a Nigeria, abin yana bambanta tsakanin wani gari zuwa wani. Gwamnatoci har yanzu basu kai ga samar da tashoshin mota na zamani da suka dace da rayuwar karni na 21 ba, zaka yi mamaki idan ka zagaya jihohinmu kaga inda ake kira tashoshin mota saikayi mamaki, kayi zaton har yanzu muna rayuwa a karni na goma sha uku ne.

An bar mutane suna rayuuwa sasakai, ba tare da kiyaye ka’ida da doka ba. An samar da tashoshin mota ne domin amfanin jama’a na yau da kullum, amma hukumomi da ya kamata su maida hankali wajen ganin lallai masu motocin sufuri suna amfani da wadannan tashoshin mota ko dan ingantar samun kudin shigar kananan hukumomi da jihohi, amma abin ba haka yake ba. Ga tasha an samar, amma masu diban fasinja, basu cika son shiga tasha ba sai dole, haka suma, fasinjoji masu hawa mota basa son shiga tasha su hau mota. An bar mutane kara zube.

Maimakon hukumomi su tilastawa masu motocin sufuri amfani da tashoshin mota, da tilasta masu hawa mota zuwa tasha su hau mota, sai aka bar abin taci barkatai, kowa yana yin yadda yaga dama. Da yawan fasinjoji na yin korafin yadda da dama daga cikin masu motocin sufuri kan ci zarafinsu, ko kin mutuntasu a matsayinsu na abokan mu’amala. Mai mota ya zagi fasinja, akan abinda bai taka kara ya karya ba, ko kaga dan kankanin yaro sabo da shi kwandasta ne, ya samu babban mutum yana ruga masa ashariya, kuma ba abinda zai faru. Wanda wannan ba daidai bane.

Tilas ne sai an dawo da bin doka da kuma tsari da da’a a rayuwar yau da kullum ta jama’a. Gwamnatoci musamman na jihohi su samar da tashoshin mota na zamani da suka dace da rayuwar yau da kullum, domin ingantawa mutane sha’anin sufuri da sauransu. Sannan tilas gwamnatoci su tursasawa masu motocin sufuri na yau da kullum su dinga amfani da tashar mota domin dauka da sauke fasinja. Ba daidai bane abar mutane suna samarwa da kansu tashoshin mota na babbu gaira bare dalili. Mutane su tsaya inda suka ga dama su hau mota, sannan su sauka inda suka ga dama. Inda duk aka cigaba ba irin wannan tsarin ake bi ba. Dole ne ya zama akwai ka’aida, kuma an sanyawa mutane kiyaye wannan ka’idar wajen hawa ko sauka daga motocin haya.

Hakazalika, masu baburan nan mai kafa uku, da ake kira Adaidaita Sahu a kano, ko Keke nafef a Kaduna. Suma suna bukatar samar musu da tashoshi domin samar da tsari a harkar sufinsu, ba daidai bane suma ace an barsu suna abinda suka ga dama, babu wani tsari akansu, in ma kaga wani tsari a tare da su daga hukuma, to bai wuce na karbar haraji ba. Amma karewa mutane walwala ko mutunci sam babu wani abu mai kama da haka. Zaka sha mamaki, idan kaga yadda masu tuka irin wannan Babura ke yin tukin ganin dama akan tituna, su zagi wanda duk suka ga dama, ko wanda yayi musu kuskure, su yi tuki son ransu, ba tare da tunanin akwai wata doka da zata yi aiki akansu ba.

Idan mutum ya kasance mai zafin rai ne, to kusan kullum sai ya hadu da takaicin masu Adaidaita sahu. Domin galibinsu matasa ne, kuma sun koyi tuka babur dinne a titi, basu san, ka’idar amfani da hanya ba, basu san ka’idar yin kiliya ko shan kwana ba, suma kuma wasu masu motocin da yawa basu san wadancan ka’idojin ba, dan haka sai ake rayuwar kare a karofi. Babu wani wanda yake mutunta kowa, kowa na takama da hanya, ba tare da saurarawa dan uwansa ba, ko daga kafa, kowa bai isa ba. Wannan duk laifi ne da hukumomi suka dauki kaso mafi tsoka a cikinsa, domin su ne a hakku, na su samar da tsarin da zai dadadawa kowa, tsakanin mai babur da maimota da kuma masu hawa mota ko babur dama masu ababen hawa nasu.

Yana daga cikin abubuwa na sakacin hukumomi shi ne rashin samar da kyakkyawan tsarin amfani da hanyoyin ababen hawa. Ga hukumomin kula da hanyoyi da masu lura da masu ababen hawa, amma kadan ne ke aikinsu yadda ya dace. Domin hukumomin gwamnati sunfi maida hankali akan abinda ya shafi cin tara ko karbar haraji, a maimakon aikin kula da ingancin hanyoyi da kuma tabbatar da cewar mutane suna amfani da hanyoyi ba tare da sun cutar da wasu ba. Amma galibi akasi ne ke faruwa.

Mutane na yiwa kansu tsari ne yadda suka ga dama. Basa mutunta dokokin amfani da hanyoyi, su kuma hukumomin basa sanya mutane su fahimci abinda ke kansu na kiyaye doka da ka’ida ba. A dinga tare motoci babu gaira babu dalili akan hanya, a cutar da mutane masu amfani da hanyar, sannan a cutar da wanda aka tsare. Sau da dama, idan anga matsala ta auku, ya kamata a dubi me ya samar da ita, kuma tayaya ta auku, ayi kokarin magancewa daga tushe, amma sam ba’a lura da wannan sai dai kawai ayi batun cin mutum tara.

Zaka ga yadda dogarawan hanya kan tare motocin da suka yi lodi fiye da kima, ana cin tararsu. Da ya kamata ne, a duba musabbabin faruwar abin. Tayaya direba ya yi lodin day a wuce ka’ida kuma ya hau titi? Asali ina tashoshin mota, wanda hakkin su ne su tabbatar da cewar masu motoci basu dauki kaya fiye da kima ba a motocinsu. Wannan zai tabbatar maka irin masu wannan daukar kaya fiye da kima, basa yin amfani da tashoshin mota na hukuma, suna amfani ne da tashoshin da suka tsarawa kansu, su dauki kaya a inda suke so, su sauke kaya a inda suka ga dama. Maganin irin wannan matsalar yana da alaka da samar da tashoshin mota na zamani, wanda suka kunshi duk wasu injina da zasu auna adadin kayan da mutum yake dauke da su, da kuma adadin kayan da mota zata iya dauka.

Abin mamaki, kaga an laftawa karamar mota kaya fiye da kima, kuma ka samu mutane sun hau saman kayan ana zuba mugun gudu da su, a irin wannan ne, daga zarar hadarin mota ya auku sai kaji anyi hasarar rayuka masu yawa. Duk wannan yana faruwa ne sakamakon sakacin hukumomi. Asalima akwai motocin da aka yisu domin daukan kaya wato “Goods Only” ma’ana kaya kawai. To amma irin wannan motocin ne zaka ga an lafta musu kaya da ya shige kimar abinda zasu dauka, sannan kuma an dora mutane a saman kayan.

Akwai kuma, motocin da zaka ga, na sufuri ne, amma a haka zaka ga ana jibga musu kaya, sannan a zuba mutane. Ko kuma motar da aka yi a ka’ida zata dauki mutum hudu banda direba, amma sai a zuba mata mutum shida, kuma hukumomi suna kallo anki tsawatarwa ko daukar matakin da ya dace, ai ba daidai bane, abar masu mota na daukar fasinja yadda suka ga dama, su loda mutane kamar kayan wanki wani kan wani.

Haka nan suma masu tuka irin manyan motocin nan masu sufiri daga wani garin zuwa wani, suna daukar kaya fiye da kima, kuma a inda suka ga dama, wani zubin su kashe titi suna lodi ba tare da kiyaye hakkin mutane masu amfani da hanyar ba. Ko su kashe hanya sabida an batawa wani daga  cikinsu rai, ko anyi masa ba daidai ba. Lallai suma, ya kamata, hukumomi su kawo tsarin da ya dace akansu. A hana musu shigowa cikin gari a lokacin da mutane suke tsaka da hada-hadar yau da kullum, a sanya su su dinga daukar kayan da bai wuce kima ba.

Amma abin takaici, da tsakar rana, sai kaga mai babbar mota ya dauko siminti buhu dari shida ya biyo kan titin da ake hada-hada da tsakar rana, duk ya batawa mutane rai, kuma ana kallonsa sai dai wani zubin kaga ana binsu ana cin tarar da bata shiga aljihun gwamnati. Wadannan kadan ne daga cikin irin abubuwa na rashin tsari da rashin son bin ka’ida da mutane suke yi musamman ta fuskar sufuri da kuma ababen hawa. Muna fatan hukumomi zasu yi abinda ya dace a harkar sufuri a fadin jihohin kasar nan.