
Hukumar kula da sadarwa ta kasa, NCC, –hta sanar da ranar 14 ga watan Satumba a matsayin ranar karshe ta hada lambobin waya da lambar shedar katin dan kasa ta NIN.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, NCC ta umarci dukkan kamfanonin layuka da su kammala tantancewa da hade lambobin wayoyi da NIN a ranar 14 ga watan Satumba na 2024.
Hukumar ta ce layukan waya sama da Miliyan 153 ne suka hade da NIN dinsu inda aka samu karuwa da kaso 96 idan aka kwantanta da kaso 69.7 a watan Janairu na wannan shekarar.
“Domin tabbatar da ana bin dokar hade lambobin waya da NIN, NCC ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa su kammala aikin tantancewa da hade lambobin layuka da NIN zuwa ranar 14 ga watan Satumba na 2024″, inji hukumar.
” Daga ranar 15 ga watan Satumba na 2024, babu wani layi da zai dinga aiki a Nijeriya ba tare da NIN ba.
“A yayin da muke tunkarar matakan karshe, NCC na neman karin hadin kai daga dukkan ‘yan Nijeriya wajen cimma burin bin dokar kaso 100”.