
Hukumar Hana sha da Fasa-kaurin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA ta ce jami’anta sun kai sumame shagunan dillancin miyagun ƙwayoyi guda biyu a Jihar Legas, inda su ka kama mace mai ɗauke da juna-biyu, Eze Joy Chioma da tabar wiwi samfurin skunk.
A sanarwar da kakakin hukumar na ƙasa, Mahmud Isa Yola ya rabawa manema labarai a a yau Lahadi, hukumar ta ce wiwi ɗin an shigo da ita ne ta haramtacciyar hanya.
Yola ya ce Chioma, mai shekaru 27 ta shiga hannun jami’an hukumar ne a ranar 17 ga watan Disamba a lokacin da su ka kai sumame shagonta da kuma gidanta da ke a Ojo, cikin garin Legas.
Ya ƙara da cewa, a wurin da aka kama Chioma an yi nasarar kama wani mai suna Michael Oroke ɗauke da ƙwaya mai nauyin kilo 29.
Kazalika, in ji Yola, NDLEA ta kama mutane huɗu, ciki har da dattijo mai shekaru 62 ɗauke da ƙwayoyi na Tramadol guda 182,000.
Ya ce a ranar 16 ga watan Disamba kuwa, jami’an na NDLEA sun kai sumame a wata maɓoyar mashaya da ke Abule-Egba du ka a cikin garin na Legas inda aka kama mutane huɗu da su ka haɗa da Basset Emmanuel, Ezekwem Lawrence, Mohammed Aliyu, da kuma Suwidi Isiaku ɗauke da ƙwayoyin Tramadol har kimanin 182,000.
Sanarwar ta ƙara da cewa a sauran jihohi da hukumar ta kai sumame a wurare daban-daban da suka hada da jihohin Ribas, Kogi, Benue, Anambra, Edo, Ikiti da kuma ondo, ta kama miyagun kwayoyi sama da kilogram 4,000
Shugaban hukumar, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), OFR, ya jinjinawa jami’ai da su ka nuna hazaka a jihohi guda 9 da aka samu wadannan nasarori, inda ya kuma bukace su da su kara kaimi.