Home Labarai Nijar: Nigeria ta yaba da sakin mai-ɗakin Bazoum daga hannun sojoji

Nijar: Nigeria ta yaba da sakin mai-ɗakin Bazoum daga hannun sojoji

0
Nijar: Nigeria ta yaba da sakin mai-ɗakin Bazoum daga hannun sojoji

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya yaba da sakin matar shugaban Nijar, Muhammad Bazoum tare da ɗan sa daga gidan yari.

Iyalan Mista Bazoum dai sun kasance a ƙarƙashin ɗaurin talala tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023, wanda sojoji su ka yi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimaki na musamman ga ministan kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa, Alkasim Abdulkadir, a Abuja a yau Talata.

Ya ce Tuggar, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin sulhu na kungiyar ECOWAS, ya ce wannan mataki ne mai kyau na dawo da zaman lafiya a Nijar da ma yankin baki daya.

Tuggar ya jaddada yin kira ga gwamnatin da Janar Abdourahamane Tchiani ke jagoranta, da ta gaggauta sakin Mohammed Bazoum daga hannun ta, tare da ba shi damar tafiys zuwa wata kasar a matsayin wani mataki na ci gaba da tattaunawa kan ɗage takunkumin da aka ƙaƙabawa ƙasar.

A cewar Tugger, sakin Bazoum zai kuma haifar da mika mulki ga tsarin dimokuraɗiyya domin amfanin al’umma, zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijar da kuma yankin.