
Karamin ministan ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayya, Aliyu Abdullahi, ya ce ƴan Najeriya na shanye kimanin lita biliyan 1.6 na madara da dangogin ta a duk shekara.
Abdullahi, wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai a jiya Asabar a Abuja yayin bikin ranar madara ta duniya ta 2024, inda ya ce kashi 60 na madara da dangogin ta shigowa da su ake daga kasashen waje.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya rawaito cewa, 1 ga watan Yuni, ita ce ranar da aka kebe a duniya domin bikin ranar madara ta duniya.
Ya ce, a cewar babban bankin Najeriya, Najeriya na kashe dala biliyan 1.5 a duk shekara wajen shigo da kayayyakin madara cikin ƙasar.
“Wannan ya faru ne saboda gibin da muka samu a fannin noma wanda ya kai kusan kashi 60 cikin 100 yayin da ‘yan Najeriya ke shanye lita biliyan 1.6 na madara da dangogin ta a duk shekara.
“Burin da shugaban kasa Bola Tinubu ke da shi shi ne mu samu haɓɓakar noma kasa har ma ta kai ga fitar da kayayyakin gona zuwa kasashen Afirka a karkashin yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci ta Afrika (AfCFTA).
“A bisa wannan shirin na ba da fifiko ne, daukar matakan da suka dace don sauya fannin kiwo musamman tsarin kiwo don samun abinci da abinci mai gina jiki ba wai kawai ya zama wajibi ba amma wata buƙata ce ta gaggawa a kasa,” in ji shi.