Home Labarai Ƴan Nijeriya miliyan 26.5 ka iya faɗa wa halin yunwa a 2024 saboda ƙarancin abinci — Rahoto

Ƴan Nijeriya miliyan 26.5 ka iya faɗa wa halin yunwa a 2024 saboda ƙarancin abinci — Rahoto

0
Ƴan Nijeriya miliyan 26.5 ka iya faɗa wa halin yunwa a 2024 saboda ƙarancin abinci — Rahoto

Wani rahoto da cibiyar Cadre Harmonize (CH) ta fitar ya nuna cewa kimanin mutane miliyan 26.5 a jihohi 26 na Najeriya za su fuskanci matsalar karancin abinci tsakanin watan Yuni da Agustan 2024.

An gabatar da sakamakon binciken ne a wani taro na masu ruwa da tsaki da Ma’aikatar noma da ci gabanal’umma ta Jihar Kwara tare da hadin gwiwar CH da sauran abokan hulda suka shirya.

Rahoton ya bayyana cewa mutanen da ake tsammanin za su fuskanci yunwa sun hada da ‘yan gudun hijira a jihohin Zamfara da Sokoto da kuma Borno.

Da ya ke jawabi a wajen taron, babban sakataren ma’aikatar, Isiaq Oloruko-oba, ya bayyana cewa irin wadannan rahotannin na fito da mawuyacin hali da rashin abinci da abinci mai gina jiki da kasar ke fuskanta.

Ya bayyana cewa yana da matukar muhimmanci ga masu mahukunta su tsara tun kafin irin wannan hatsarin da ke kunno kai tare da samar da mafita mai dorewa.

A cewarsa, taron ya baiwa dukkan masu ruwa da tsaki damar yin shawarwari kan hanyar da za a bi.

Ya nanata kudurin gwamnatin jihar na ganin an baiwa masu ruwa da tsaki musamman manoma karfi tare da samun tallafin da ya kamata domin tabbatar da wadatar abinci a jihar.