Home Kasuwanci Ƴan Nijeriya sun kashe Naira Tiriliyan 1.25 kan kiran waya da data a watanni 6 — NCC

Ƴan Nijeriya sun kashe Naira Tiriliyan 1.25 kan kiran waya da data a watanni 6 — NCC

0
Ƴan Nijeriya sun kashe Naira Tiriliyan 1.25 kan kiran waya da data a watanni 6 — NCC

 

 

Masu amfani da wayar sadarwa sun kashe aƙalla Naira Tiriliyan 1.25 wajen kira da data a cikin watanni shida na farkon shekarar 2022.

Hakan na kunshe ne a cikin rahoton kudi na rabin shekara na MTN Nigeria da Airtel Africa, inda hakan yai daidai da karin kashi 17.77 daga Naira Tiriliyan 1.06 da aka kashe wajen kira da data a irin wannan lokacin a shekarar 2021.

A cikin watanni shida na farkon shekarar 2022, kamfanin MTN ya bayyana cewa ya samu Naira biliyan 850.33 daga waya da data, karin kashi 18.50 cikin 100 daga Naira biliyan 717.56 da ya samu a irin wannan lokacin a shekarar 2021.

Kamfanin na Airtel ya bayyana cewa aikin da ya ke yi a Nijeriya ya samu Naira biliyan 399.39 (Dalar Amurka 931m) daga waya da amfani da data, karin kashi 16.23 cikin 100 daga Naira biliyan 343.63 (Dalar Amurka 801m) da ya samu a irin wannan lokacin shekarar 2021.

Binciken rahotannin ya nuna cewa kudaden shiga na data sun samu haɓɓaka da sauri fiye da kuɗaɗen shiga da a ka samu a kiran waya.