Home Labarai NIMET ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a jihohin Arewa 5 da Abuja

NIMET ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a jihohin Arewa 5 da Abuja

0
NIMET ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a jihohin Arewa 5 da Abuja

 

 

 

Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa, NIMET ta yi hasashen fuskantar kakkarfan ruwan sama na tsawon kwanaki 4 babu kakkautawa a wasu jihohin arewacin kasar 5, da kuma birnin Abuja fadar gwamnatin kasar.

Cikin rahoton hasashen yanayin da hukumar ta NIMET ta fitar, ta ce jihohin da za su fuskanci wannan ruwa na tsawon kwanaki 4 ba tare da kakkautawa ba sun haɗa da Kaduna, Neja, Bauchi,Plateau da kuma jihar Nassarawa, baya ga birnin Tarayyar kasar.

Rahoton na NIMET ya kuma yi hasashen fuskantar madaidaicin ruwan sama a wasu jihohin Najeriya daga kudanci da arewaci da suka haɗa da, Kwara da Oyo da Kogi da Ekiti da Ondo baya da Sokoto da Katsina da Zamfara.

Sauran jihohin da za su fuskanci mamakon ruwan sun hada da Kebbi da Kano da Jigawa da Yobe Borno da Gombe da Adamawa da Taraba da Benue da Cross River da Akwa Ibom kana Ebonyi da Enugu da Abia da Imo da Anambra da Rivers da Edo da kuma jihar Delta.

Hukumar ta NIMET ta bukaci daukar matakan gaggawa don kaucewa fuskantar ambaliya musamman la’akari da cewa dukkanin jihohin da ta lissafa kama daga wadanda za su fuskanci mamakon ruwan da wadanda za su fuskanci madaidaici da kuma kakkarfa, kowannensu zai zo da kakkarfar iska.