Home Labarai Ortom ya ƙaddamar da hukumar tsaro ta Jihar Benue

Ortom ya ƙaddamar da hukumar tsaro ta Jihar Benue

0
Ortom ya ƙaddamar da hukumar tsaro ta Jihar Benue

 

 

 

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ya ƙaddamar da hukumar tsaron sa-kai ta jiha a jiya Alhamis.

Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamar da rukunin farko na jami’an tsaron guda 500, Ortom ya ce dole ce ta sanya ya ƙirkiri ƴan sintirin na sa-kai domin magance ayyukan ƴan ta’adda a jihar.

“Dole ce ta sanya mu ƙirkiri wannan hukuma mai tsada. Ba dan ayyukan ƴan ta’adda a ƙasar mu ba da ba mu yi wannan ba.

“Benue wacce ta ke da kirari mai kyau na cewa ita ce kwandon kayan abinci ta ƙasa, wacce ta ke da kasa mai kyau da ruwa ingantacce, ta faɗa hannun ƴan ta’adda .”waɗannan ƴan ta’addan mashaya jini sun kashe ɗaruruwan al’ummar ta hanyar kisan gilla, fyade, ƙone-ƙone da sauran ayyukan ɓatagari,”

A cewar sa, ayyukan ƴan ta’adda sun yi sanadiyar ɗaiɗaita sama da mutane miliyan 1.5 inda su ka koma zama a sansanin ƴan gudun hijira a jihar.