Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo tare da rakiyar Ministan sufuri na Najeriya Rotimi Amaechi sun kaiwa tsohon Shugaban kasa Olushegun Obasanjo ziyara a Gidan gonarsa dake Otta a jihar Ogun.

Ba dai a bayyana dalilan wannan ziyara ba, amma bayanai sun nuna tana da nasaba da zaben 2019 dake tafe nan da kwanaki dari masu zuwa.

Tuntuni dai Obasanjo yake sukar salon Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Inda ya rubuta wata wasika yana mai baiwa Shugaban shawara da kada ya nemi tsayawa takara a zaben 2019.