Sshugaban Kwamitin riko na jam'iyyar PDP, Sanata Ahmad Mohammed Makarfi

Jam’iyyar PDP mai hamayya, ta bayyana rashin gamsuwarta da matakin da Gwamnatin Buhari ta dauka na korar su Babachir da Oke daga aiki ba tare da bayyanawa al’ummar Najeriya rahoton kwamitin binciken da ta kafa a kansu ba. Jam’iyyar ta bayyana cewar, wannan dodo rido ne ake yiwa ‘yan najeriya game da wannan batu.

PDP ta bayyana hakan ne ta bakin kakakin kwamitin riko na jam’iyyar karkashin jagorancin Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, wata Yarima Dayo Adeyeye, a ranar litinin a harabar sakatariyar jam’iyyar dake babban birnin tarayya Abuja.

Idan ba’a manta ba, a litinin dinnane Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayar da sanarwar korar dakataccen sakataren Gwamnatin tarayya Babachir David Lawal daga aaiki tare da shugaban hukumar NIA Ayo Oke.

PDP ta bayyana cewar, korarsu ba tare da bayyana ainihin rahoton kwamitin da Shugaban ƙasa ya kafa karkashin jagorancin mataimakinsa Yemi Osibanjo ba, kamar shiga ɗaka da kare ne. Kuma wannan ba abin yadda bane.

‘Yan Najeriya sun jima suna dakon irin matakin da Shugaban kasa zai ɗauka kan wannan badakala da ta shafi manya manyan makusantansa ta fuskar aiki.

“Sam sam bamu yarda da wannan mataki da shugaban kasa ya dauka a dukunkune ba, tilas a fito a yiwa ‘yan Najeriya bayanin, kuma a bar shariah tayi aikinta akan mutanan da aka kama da laifi, ba wai kawai a sallame su ayi shiru ba”.

“dan haka, tilas a tura wadannan mutane zuwa gaban hukumar EFCC domin cigaba da bincikarsu, tunda Shugaban kasa yaki bayyanawa al’umma asalin llaifin da aka same su da shi”.

Rahoton kwamitin Yemi Osibanjo ya kamata ya zama a bayyane, ‘yan najeriya su gani su karanta, dan su san ainihin laifin da mutanan da aka kora suka yi.

PDP ta ci gaba da cewar, Gwamnati karkashin jam’iyyar APC na yin rufa rufa kan batun cin hanci da rashawa a Najeriya, musamman abinda ya shafi wasu manya daga cikin Gwamnatin.

Sun ce, tilas ne hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su binciki Babachir da Oke dan sanin hakikanin laifin da suka aikta, sannan su fuskanci kuliya.

Wannan babban laifi ne da ake zargin wadannan mutane da aikatawa, ba wai kawai korarsu Shugaban kasa zai yi yayi shiru ba, tilas ayi bayani, dan ba zamu zauna, muna tafawa shugaban kasa a irin wannan dukunkune da yayi ba.

Mun gamsu da tsarin demokaradiyya da kuma kundin tsarin mulki da ya baiwa kowanne dan kasa dama, sannan babu wani batun boye boye da za’a yiwa al’ummar Najeriya ba.

Wannan sam ba adalci bane, su Babachir da Ayo a kore su kawai ba tare da daukar wani mataki akansu, bayan kuma sauran mutane Gwamnati na mika su wajen hukumomin bincike dan gurfanar da su gaban shariah.

Kamfanin dillancin Labarai na Najeriya ne ya ruwaito wannan rahoto. Ko me zaku ce akansa?