32.6 C
Abuja
Friday, June 2, 2023

PDP ta dakatar da jami’an ta na mazaɓa a Benue saboda dakatar da Ayu

Must read

Kwamitin Koli na Jiha, SWC, na jam’iyyar PDP, a Benue, ya dakatar da jami’anta a mazaɓar Igyorov, saboda dakatar da tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu.

Dakatarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP, Mista Isaac Mffo tare da wasu mutane 12 a Makurdi.

A cewar SWC ɗin, an dakatar da shugabannin mazaɓar ne na tsawon wata guda har sai an dauki matakai da su ka dace don dawo da zaman lafiya, daidaito da doka da oda a cikin jam’iyyar.

Ya bayyana cewa SWC a wannan lokaci ne za ta gudanar da al’amuran jam’iyyar a shiyyar, inda ta kara da cewa matakin ya kasance mafi alheri ga jam’iyyar.

Sanarwar ta kuma umurce su da su mika duk wasu takardu da sauran kayayyakin jam’iyyar da ke hannun su zuwa SWC na jam’iyyar nan take.

Ya kara da cewa daga yanzu za su daina aiki a ofisoshin da suke rike da su kafin a dakatar da su, inda suka dage cewa an dauki matakin ne domin dawo da hayyacin jam’iyyar a unguwar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an sanar da dakatar da Ayu ne a ranar 28 ga watan Maris a karamar hukumar sa ta Igyorov da ke karamar hukumar Gboko a jihar Benue.

Vangeryina Dooyum, sakataren mazaɓar Igyorov, wanda ya wakilci shugaban jam’iyyar, Kashi Philip, ya ce an dakatar da Ayu daga jam’iyyar ne sakamakon ayyukan da ya yi na zangon ƙasa ga jam’iyyar yayin zabukan da aka gudanar kwanan nan a fadin Najeriya.

More articles

Latest article

X whatsapp