
Dr Adetokunbo Pearse, ƙusa a jam’iyyar PDP a Legas, kuma tsohon mamba, kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na 2023, Atiku Abubakar, ya ce har yanzu jam’iyyar ta adawa na nan da ran ta kuma a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.
Pearse, wanda tsohon dan takarar shugabancin jam’iyyar na kasa ne kuma dan takarar gwamna a jihar Legas, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN a yau Alhamis cewa jam’iyyar ba ta mutu ba kamar yadda ake mata kallo.
Ya ce: “Har yanzu PDP na nan daram. Ba share batun PDP a Najeriya ba. Idan aka dubi yanayin kasa, PDP har yanzu tana da karfi sosai a matsayi na biyu a majalisar kasa.
APC tana da gwamnoni kusan 20, muna da gwamnoni kusan 14 yayin da sauran jam’iyyu ke da guda biyu.
“Idan muka je Majalisar Dokoki ta kasa, muna da karfin lamba na biyu tare da watakila kashi 38 zuwa kashi 40 na mambobin.”
Pearse, ya ce karfin jam’iyyar PDP a jihar Legas wani lamari ne na daban, domin jam’iyyar Labour ta kori PDP ta zama ta biyu da rata mai tsawo daga APC mai mulki.