Home Siyasa 2023: PDP ta nemi a soke takarar Gwamna Abdulrazaq bisa zargin takardun bogi

2023: PDP ta nemi a soke takarar Gwamna Abdulrazaq bisa zargin takardun bogi

0
2023: PDP ta nemi a soke takarar Gwamna Abdulrazaq bisa zargin takardun bogi

 

A yau Alhamis ne jam’iyyar PDP ta roki wata babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta bayar da umarnin haramtawa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Kwara shiga zaben gwamnan jihar a shekarar 2023 bisa zarginsa da amfani da takardun bogi.

Jam’iyyar PDP, a wata takardar ƙarar da ta gabatar a gaban mai shari’a Inyang Ekwo, ta kuma yi roƙon da kotu ta bada umarnin hana jam’iyar APC tsayar da ɗan takarar gwamna a jihar a zaɓen 2023.

Jam’iyyar a cikin karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/1324/2022 da lauyanta Paul Erokoro, SAN, ya shigar a ranar 4 ga watan Agusta, ta kuma bukaci kotun da ta ba da umarnin umurtar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da soke sunan Abdulrazaq a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Kwara a 2023.

Yayin da PDP ce mai shigar da kara, INEC, Gwamna Abdulrazaq da APC ne waɗanda a ke ƙara na 1 zuwa 3.

Jam’iyyar ta tambayi ko ta hanyar Sashe na 177 (D), 182 (1) (j) da 285 (14) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (kamar yadda aka gyara); Sashe na 29 (2) da na (4) na dokar zabe, 2022, takardar Abdulrazaq na goyon bayan bayanansa na sirri (Form EC9) da kuma takardun da hukumar INEC ta buga na kunshe da bayanan karya don taimaka masa wajen neman cancantar neman takarar gwamna a 2023. a cikin jihar.

Ƙarar, wacce aka saurara a yau Alhamis, mai shari’a Ekwo ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Oktoba.