Home Labarai Rage cunkoso: Gwamnatin tarayya ta saki fursunoni 150 a gidajen gyaran hali na Kano

Rage cunkoso: Gwamnatin tarayya ta saki fursunoni 150 a gidajen gyaran hali na Kano

0
Rage cunkoso: Gwamnatin tarayya ta saki fursunoni 150 a gidajen gyaran hali na Kano

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da sakin fursunoni 150 a jihar Kano.

Da ya ke jawabi a wajen taron gabatar da fursunonin, wanda aka gudanar a babbar cibiyar tsaro a Kano a yau Alhamis, Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Ojo, ya ce fursunonin 150 na cikin guda dubu 4,068 da za a saki a fadin kasar.

A cewar Mista Ojo, sakin fursunonin na daga cikin kokarin gwamnatin tarayya na rage cunkoso a gidajen gyaran hali, ƙarƙashin kudirin shugaba Bola Tinubu nas “Sabuwar Nijeriya”.

Ministan ya bayyana cewa an saki wadanda suka ci gajiyar bayan sun yi zaman gidan yari na wa’adi daban-daban saboda sun kasa biyan tara ko diyya.

Ya bayyana cewa, wasu masu hannu da shuni, kungiyoyi da daidakun mutane ne suka tara Naira miliyan 585, a matsayin wani bangare na ayyukan cigaban al’umma, na sakin fursunonin a fadin kasar, inda ya ce daga cikin kudaden an kashe Nair miliyan 13 da dubu 436 wajen sakin fursunonin 150 a Jihar Kano.

Tun da fari, a nasa jawabin, Kwanturola na cibiyoyin gyaran hali na jihar Kano, Suleman Inuwa, ya bayyana cewa cibiyoyin kula da cewa akwai cunkoso a gidajen yari a fadin kasar nan, dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani shiri a kwanakin baya, da nufin rage cunkoso a cibiyoyin.

Shirin, a cewar Inuwa, ta hanyar “Biyan Tara da Fansa”, ya riga ya yi tasiri sosai ga rayuwar fursunonin da dama a faɗin ƙasar.

Kwanturola ya kuma yi kira ga wadanda suka amfana da su rungumi kananan sana’o’i domin dogaro da kai.