Home Labarai Ramadan: Gwamnatin sojin Nijar ta karya farashin shinkafa

Ramadan: Gwamnatin sojin Nijar ta karya farashin shinkafa

0
Ramadan: Gwamnatin sojin Nijar ta karya farashin shinkafa

Gwamnatin Soji mai mulki a Jamhuriyyar Nijar, ta karya farashin shinkafa da ta yi tashin gwauron zabi a watanni baya bayan nan.

Tun dai lokacin da Ƙungiyar ECOWAS ta sanya wa Nijar takunkumin karayar tattalin arziki bayan juyin mulki kusan watanni bakwai da suka gabata, farashin shinkafa ya yi tashin gwauron zabo.

Bayanai sun ce tun a wancan lokacin farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 25 ya tashi daga jikka 11 na CFA zuwa jikka 15 har zuwa 18 a wasu yankunan kasar.

Sai dai a yanzu Gwamnatin Sojin da ta kifar da Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023, ta ƙuduri cewa za a riƙa sayar da buhun shinkafar mai nauyin kilo 25 kan Jika 13 na CFA a birnin Yammai.

Haka kuma, gwamnatin ta ƙayyade farashin buhun shinkafar mai nauyin kilo 25 kan Jika 13 da dala 135 a Dosso, Jika 13 da dala 165 a Tahoua, Jika 13 da dala 185 a Maradi, Jika 14 daidai na CFA a Damagaram, Jika 14 da dala 75 a Diffa, Jika 14 da dala 25 a Agadez sai kuma jika 13 da dala 130 na CFA a Tillabery.

Malam Ayuba Djimrao, babban mai ba da shawara ga Ministan Kasuwanci na kasar, ya bayyana dalilin karya farashin shinkafar a daidai wannan lokaci.

Malam Djimrao ya ce sun ɗauki wannan ƙuduri ne domin su ceci al’umma da kuma ƙasa baki ɗaya la’akari da halin da ake ciki musamman yadda watan Azumin Ramadana ya tunkaro.

Ya ce wannan mataki da suka ɗauka zai taimaka wa al’umma su gudanar da ibadar Azumin Ramadana cikin sauƙi.

AMINIYA