28.1 C
Abuja
Sunday, April 21, 2024

Ramadan: Mustahabbi ne mata su fito Sallar dare a goman karshe – Dr. Jalo Jalingo

Must read

Jaafar Jaafar
Jaafar Jaafarhttps://dailynigerian.com/
Jaafar Jaafar is a graduate of Mass Communication from Bayero University, Kano. He was a reporter at Daily Trust, an assistant editor at Premium Times and now the editor-in-chief of Daily Nigerian.
  1. Yau Talata muna goma sha uku ga watan Ramadan, watan dukkan wani alheri. Sannan mako daya ne kacal ya rage mana mu shiga goman karshe na wannan Wata mai yawan daraja. Sannan akwai ibadu da yawa da ake kara yawaita su a cikin wadannan kwanaki na goman karshe; kamar sallolin dare cikin jama’a, da I’itikafi. A wannan rubutu namu za mu fara tunatarwa ne a kan sallolin dare cikin jama’a cikin goman karshe na wannan wata mai yawan daraja.
  2. Lalle sunnah ce wacce ake son aikatawa: Mata Musulmi su fito Masallatai su yi Qiyaamu Ramadan a goman karshe cikin jama’a, watau jam’i kamar yadda mutanenmu suka fi kira.

Imam Ibnu Khuzaimah wanda yau da mutuwarsa shekaru dubu daya da dari daya da ishrin da bakwai (1,127) ya ce cikin sahihinsa mai suna Mukhtasarul Mukhtasar 3/339: ((باب استحباب صلاة النساء جماعة مع الامام في قيام رمضان مع الدليل على ان قيام رمضان في جماعة أفضل من صلاة المرء منفردا في رمضان)). Ma’an((Babin mustahabbancin sallar mata a cikin jam’i tare da Liman a cikin Qiyaamu Ramadan, da kuma hujjar cewa yin Qiyaamu Ramdan a cikin jam’i shi ne ya fi a kan mutum ya yi salla shi kadansa cikin Ramadan)).

Sheikh Hamzah Bin Faayee ya ce cikin littafinsa Talaa’i’us Sulwaan shafi na 138 ((فالخلاصة ان خروجهن للتراويح مسنون ومحمود )). Ma’ana: ((A takaice dai lalle fitowarsu saboda yin sallar Taraawiihi sunna ce kuma abin godewa)).

  1. Hujjar mustahabbancin fitowar Mata Masallatai domin sallatar Qiyaamu Ramadan cikin jam’i a goman karshe shi ne: Hadithin Sahabi Abu Zarr Hadithi na 1377 cikin Abu Dawud, na 806 cikin Tirmizii, na 1364 cikin Nasaa’ii, na 1327 cikin Ibnu Majah, na 21,447 cikin Musnadu Ahmad, na 2206 cikin Sahihu Ibnu khuzaimah, na 4042 Musnadu Bazzar, na 7706 cikin Musannafu Abdirrazzaq cewa shi Abu Zarr ya ce:-

((صمنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم رمضان فلم يقم بنا شيءا من الشهر حتى بقي سبع فقام بنا حتى ذهب ثلث الليل فلما كانت السادسة لم يقم بنا، فلما كانت الخامسة قام بنا حتى ذهب شطر الليل، فقلت يا رسول الله! لو نفلتنا قيام هذه الليلة؟ قال: فقال: ان الرجل اذا صلى مع الامام حتى ينصرف حسب له قيام ليلة. قال: فلما كانت الرابعة لم يقم، فلما كانت الثالثة جمع أهله ونساءه والناس فقام بنا حتى خشينا ان يفوتنا الفلاح)).

Ma’ana: ((Mun yi azumin Ramadan tare da Manzon Allah mai tsira da amincin Allah bai mana limancin kome ba a sallar qiyaamul laili cikin watan sai da ya rage kwana bakwai watan ya kare sai ya yi mana limancin qiyaamul laili saida kashi daya cikin na dare ya tafi, a dare na shida da ya rage bai yi mana limancin qiyaamul laili ba, a dare na biyar da ya rage sai ya yi mana limancin qiyaamul laili har saida rabin dare ya tafi, to sa na ce: Ya Manzon Allah! Me ya sa ba ka yi mana qiyaamul lili na dukkan daren ba? Sai ya ce: Hakika idan mutum ya yi salla tare da liman har dai limamin ya gama sallar to kuwa za a ba shi ladan wanda ya sallaci dukkan daren ne. Ya ce: a dare ba hudu da ya rage bai yi mana limancin qiyaamul laili ba, a dare na uku da ya rage sai ya taro iyalansa, da matansa na aure, da kuma mutane ya yi mana limancin qiyaamul laili har saida muka ji tsoron kada yin sahur ya kubuce mana)). Wannan Hadithi Albaanii da sauransu sun inganta shi.

– Ya zo cikin riwayar Tirmizii ((Ya kira iyalansa, da matansa na aure ya yi mana limancin qiyaamul laili)).

– Ya zo cikin riwayar Nasaa’ii ((Sai ya aika zuwa iyalansa, da matansa na aure, ya tara mutane ya yi mana limancin qiyaamul laili)).

– Ya zo cikin riwayar Bazzar ((Sai ya aika zuwa ga iyalansa, da matansa na aure suka hadu sannan ya yi mana limancin qiyaamul laili)).

– Ya zo cikin riwayar Abdirrazzaq ((Ya aika zuwa ga iyalansa mutane kuma suka taru sannan ya yi kana limancin qiyaamul laili)).

  1. Ke nan tunda cikin sashin wadannan goman karshen Annabi mai tsira da amincin Allah ya tara iyalansa da matansa na aure da kuma sauran jama’a a cikin masallacinsa ya yi musu limancin qiyaamul laili, wannan yana tabbatar mana da cewa lalle maza da mata su taho masallaci a darairan goman karshe domin yin qiyaamu Ramadan cikin jima’i shi ne ya fi falala,shi ne abin so; saboda shi ne Annabi Mai tsira da amincin Allah ya zaba wa al’ummarsa; shi kuwa Annabi mai tsira da amincin Allah ba ya zaba wa al’ummarsa wani abu sai in abin shi ne ya fi falala a gurin Allah Madaukakin Sarki.

Ibnu Qudaamah ya ce cikin Al-Mugni 7/334 :-

((ولا يشتغل النبي صلى الله عليه وسلم وأصحابه الا بالافضل)).

Ma’ana: ((Annabi mai tsira da amincin Allah da sahabban shi ba sa shgalta sai da abin da shi ne ya if falala)).

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin majmuu’ul Faawaa 26/54:-

((والنبي صلى الله عليه وسلم لا ينقلهم من الفاضل الى المفضول بل إنما يأمرهم بما هو أفضل لهم)).

Ma’ana: ((Annabi mai tsira da amincin Allah ba zai cirar da su daga abu mai daraja ba zuwa ga abin da aka fi shi daraja, a’a ya kan umurce su ne da abin da shi ne mafi falala gare su)).

  1. Idan wani ya kalubalanci wannan magana tamu ya ce: ai Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce ((Mafificiyar salla ita ce sallar mutum a cikin dakin shi matukar dai ba sallar farilla ba)). Sai mu ce da shi wannan Hadithi an toge shi da hadithin Abu Zarr da muka ambata a sama, kamar yadda aka toge shi aka khassase shi da Hadithan sallar Idi, da rokon ruwa, da kusuufin Rana.  Watau sai a ce: sallar nafila a gida ita ta fi falala amma banda nafilfilin qiyaamu Ramadan a daren goman karshe, banda nafilfilin sallar Idi, da rokon ruwa, da khusufin Rana….
  2. Idan kuma wani ya kalubalance mu cikin abin nan da muka fada ya ce: ai Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Kada ku hana mata zuwa masallatai, amma kuma dakunansu su ne suka fi alheri a gare su)). Sai mu ce da shi wannan Hadithi an toge shi watau an khassase shi da hadithin Abu Zarr da muka ambata a sama kamar yadda aka khassase shi da hadithin umurtan mata da su fita zuwa masallacin Idi: masu tsarkinsu da mara tsarkinsu. Watau sai a ce: Mata su yi sallolinsu cikin dakunansu shi ne ya fi falala a gurin Allah matukar dai sallolin nan ba na Idi ba ne, matukar dai sallolin nan ba na qiyaamu Ramadan ba ne a darairan goman karshe.

Allah muke roko da Ya taimake mu har kullum. Ameen.

 

More articles

Latest article