Jam’iyyar PDP ta bayyana cewar ya sanya ranar 6 ga watan Oktoba a matsayin ranar da zata fitar da dan takarar Shugaban Kasa da zai Kara da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

’Yan takarar neman jam’iyya ta amince musu yi mata takara a 2019 sun hada da tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan Gombe Ibrahim Dankwambo.

Sauran su ne Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Attahiru Bafarawa da Ahmad Makarfi da Kabiru Tanimu Turaki da tsohon Gwamnan jihar Plateau Jonah Janga.

Ragowar sune David Alachenu Mark da Datti Baba-Ahmed da sauransu.