
Gwamnatin tarayya ta sanar da gobe Laraba, 12 ga watan Yuni, 2024 a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar dimokradiyya ta bana.
Ministan harkokin cikin gida, Hon. Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a yau Talata a cikin wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar Dr. Aishetu Gogo Ndayako ya fitar.
Ya ce, “Yayin da muke sake bikin ranar dimokuradiyya a cikin tarihin kasarmu mai daraja, bari mu yi duba kan magabatan mu da suka kafa mu da kuma tabbatar da cewa Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya, amintacciyar kasa, zaman lafiya da hadin kai.”
Yayin da ya ke taya yan Najeriya murnar wannan rana, Ministan ya bukace su da su kasance masu biyayya da tsarin mulkin dimokradiyya.
Dakta Tunji-Ojo ya sake nanata cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kuduri aniyar kawo sauyi mai kyau domin farfado da tattalin arzikin kasa da inganta tsaro.
Ministan ya yi kira ga ƴan Najeriya da abokan Najeriya da su yaba da ci gaban da aka samu, da kuma fatan samun makoma mai kyau ga Dimokradiyyar Najeriya.