Home Labarai Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta rufe kasuwannin shanu 11 a jihar

Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta rufe kasuwannin shanu 11 a jihar

0
Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta rufe kasuwannin shanu 11 a jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta sake rufe kasuwannin shanu goma sha daya a fadin jihar har sai baba-ta-gani.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Munnir Haidara ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau a jiya Alhamis.

Ya ce rahotannin tsaro sun nuna cewa ‘yan fashin jeji na amfani da wadannan kasuwanni wajen sayar da shanunsu da suka sace.

Kasuwannin da abin ya shafa a cewar kwamishinan sun hada da kasuwannin Tsafe da Bilbis a karamar hukumar Tsafe da kasuwar Jangebe da ke karamar hukumar Talata-Mafara da kuma kasuwar Wuya da ke yankin Anka.

Sauran kasuwannin sun hada da kasuwar Mujallar Diddi dake karamar hukumar Maradun, kasuwar Galadi dake karamar hukumar Shinkafi, kasuwar Mada dake karamar hukumar Gusau da Sabon Birnin Danali dake karamar hukumar Birnin Magaji.

Sauran kasuwannin Kokiya, Chigama da Nasarawar Godel duk a karamar hukumar Birnin Magaji.

Haidara ya ce gwamnatin jihar ta ga ya zama dole ta rufe wadannan kasuwannin sakamakon rahotannin tsaro da ke cewa ‘yan bindigar na hada baki da wasu marasa kishin kasa domin sayar da shanunsu da aka sace a kasuwannin.

Ya ce gwamnatin jihar ta umurci jami’an tsaro da su tabbatar da bin doka da oda tare da kama duk wanda ya karya dokar.