25.1 C
Abuja
Monday, August 8, 2022

Rashin tsaro: Masarautar Katsina ta dakatar da hawan Babbar Sallah

Must read

 

 

Majalisar Masarautar Katsina ta sanar da dakatar da Hauwan bukukuwan Sallah Babba a ranar Asabar.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata a Katsina, mai ɗauke da sa hannun mataimakin sakataren majalisar, Sule Mamman-Dee, masarautar ta ce an dakatar da hawan ne saboda yanayin tsaro da ake fama da shi a jihar.

A cewar Mamman-Dee, Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir-Usman, ya nuna matukar damuwarsa kan matsalar tsaro a sassan masarautar inda ya ce zai halarci Sallar Idi ne kawai a ranar Asabar ba tare da hawan sallah ba.

Ya bayyana cewa Sarkin ya shawarci al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.

Bikin dabar dai ya samo asali ne tun shekaru aru aru da suka gabata, Shekaru kusan biyu kenan ba’a gudanar da hawan ba, saboda matsala ta tsaro data addabi al’ummar jihar.

naija news today

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article