27.7 C
Abuja
Tuesday, January 25, 2022

Rasuwar Dakta Ahmad ta girgiza ni — Ganduje

Must read

 

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiyana cewa rasuwar fitaccen malamin addinin Musluncin nan , Dakta Ahmad Muhammad Bamba, ta girgiza shi da ma al’ummar Kano baki ɗaya.

Ganduje ya baiyana haka ne a sakon ta’aziya ta hannun kakakin sa, Abba Anwar a yau Juma’a.

“Mutuwar sa ta girgiza Kano matuƙa. Hamshaƙin malami ne da ya ke da ɗumbin ilimin addini. Malami ke da ya ke da sani mai zurfi a kan Hadisan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.

“Malami ne da ya ke amfani da majailisin karatun sa wajen yaɗa zaman lafiya tsakanin al’umma da ɗarikun addini.

“Wannan rasuwa ce da mu ke alhinin ta kuma za mu dade mu na alhini da jimami,” in ji Ganduje.

Ganduje ya yi kira ga sauran malami na jihar da su kwaikwayi irin aiyukan da ya yi wa addinin Musulunci.

“Ya kafa tushe mai ƙarfi na kiran al’umma da su karɓi addinin musulunci kuma malami ke mai aikata abubuwan da ya ke yin wa’azi a kai,”

Ganduje ya mika ta’aziyar sa ga iyalin mamacin, sannan ya yi addu’ar Allah Ya yi masa rahma , Ya kuma baiwa iyalin sa da mutanen Kano jure rashin sa.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article