Home Siyasa Rigingimun APC ba za su ɗauke hankalin mu da ga yiwa al’umma aiki ba — Ganduje

Rigingimun APC ba za su ɗauke hankalin mu da ga yiwa al’umma aiki ba — Ganduje

0
Rigingimun APC ba za su ɗauke hankalin mu da ga yiwa al’umma aiki ba — Ganduje

 

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce rigingimun APC a jihar wani salo ne na ƴam adawa domin su ɗauke hankalin gwamnati da ga ci gaba da yi wa al’ummar jihar aiyuka.

A ƴan watannin da su ka gabata ne dai rikici ya ɓarke a jam’iyar mai mulki a jihar Kano, inda ta dare gida biyu, gidan gwamna mai ci, Ganduje, da kuma tsagin tsohon gwamna, Sanata Ibrahim Shekarau.

A makon da ya gabata ne dai wata babbar kotu a Abuja ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hamza Muazu ta tabbatar da cewa ɓangaren Shekarau na jam’iyar APC ya yi sahihin zaɓe na shugabannin jam’iya a matakin karamar hukuma da mazaɓu a jihar.

Da ga nan ne kotun ta tabbatar da shugabancin Ahmadu Ɗanzago na tsagin Shekarau ta kuma umarci ɓangaren Ganduje da ya biya su Ɗanzago naira miliyan 1 sabo da ɓata musu lokaci.

Da ya ke jawabi bayan wani taro na masu ruwa da tsaki na APC a gidan gwamnatin Kano a juya Lahadi, Ganduje ya ce duk wannan rigingimun na cikin gida ne kuma za su zo ƙarshe.

A cewar Ganduje, dama domokraɗiyya ta gaji irin wannan rigingimun, in danya ƙara da cewa koma dai menene, ɓangaren shi ne da nasara.

Ya kuma cewa masu haɗa rigingimun su na yi ne domin su ɗauke hankalin gwamnatin sa da na masu riƙe da madafun iko da ga aiyukan ci gaba da su ke yi a jihar.

Ya ce wannan ba zai ɗauke hankalin gwamnatin sa ba domin a cewar sa, gwamnatin ta duƙufa ne wajen yiwa al’umma aiki domin su sharɓi romon domokraɗiyya.

Ganduje ya ce burin masu haɗa rigimar ba zai cika ba domin gwamnatin sa za ta ci gaba da bijiro da aiyukan ci gaba ga al’ummar jihar.

Ya kuma tabbatar da cewa an bi hanyar da domokraɗiyya ta tanada wajen fitar da ƴan takarar shugabannin jam’iyya na mazaɓa da ƙananan hukumomi.