
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi ganawar sirri da Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari a fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja a yau Juma’a.
Daily Nigerian Hausa ta gano hotunan ganawar a shafin wani hadimin Shugaban Ƙasa, Buhari Sallau da ya wallafa a shafin sa na Facebook.
Kawo yanzu dai ba a baiyana abubuwan da su ka tattauna ba, amma a na ganin ganawar na da nasaba da rikicin da Jam’iyyar APC take fuskanta a Jihar Kano.
A tuna cewa jam’iyar mai mulki ta APC ta dare gida biyu, ƙarƙashin jagorancin Ganduje da tsohon Gwamna, Sanata Ibrahim Shekarau tun bayan zaɓen shugabannin jam’iya na jiha.