
Lauyoyin da ke kare Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero kan rikicin masarauta a kotu, ƙarƙashin Abddul Muhammed ami darajar SAN sun zare hannunsu da ga kare Sarkin a gaban Babbar Kotun jiha.
Masu shigar da ƙara a shari’ar sun haɗa da Kwamishinan Shari’a na Kano, shugaban majalisar dokoki ta Kano da majalisar dokoki ta Kano.
Sun shigar da kara ta hannun lauyan su, Ibrahim Isah-Wangida kan cewa kotu ta hana Bayero da sauran sarakuna 4 daga nuna kansu a matsayin sarakuna.
Wadanda ake kara sun hada da Aminu Ado-Bayero, Nasiru Ado-Bayero Sarkin Bichi Dr Ibrahim Abubakar ll, sarkin Karaye, Alhaji Kabiru Muhammad-Inuwa, Sarkin Rano da Aliyu Ibrahim-Gaya, Sarkin Gaya.
Sauran sun haɗa da Babban Sifeton Ƴansanda na kasa, Daraktan hukumar SSS da kwamandan rundunar kare fararen hula.
Lauyoyin Bayero, a zaman kotun na yau Alhamis, sun shaida wa kotun da a dakata da sauraron shari’ar saboda sun daukaka kara har sai an saurari ƙarar da suka daukaka.
Ya ce da safiyar Alhamis aka kai musu takardar shari’ar inda ya nemi da kotun da ta dakatar har sai sun yi nazari sun maida martani, rokon da kotun ta ki amincewa da shi.
Shine daga bisani sai ya sanarwa da kotun cewa sun zare hannun su daga kare Bayero.