Home Labarai Rikicin masarautar Kano na damuna kuma ƴan siyasa ne su ka haifar da shi – Shekarau

Rikicin masarautar Kano na damuna kuma ƴan siyasa ne su ka haifar da shi – Shekarau

0
Rikicin masarautar Kano na damuna kuma ƴan siyasa ne su ka haifar da shi – Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce ya damu da rikicin masarautar Kano sai dai ya ce bazai tsoma baki kan rikicin ba.

Tsohon Gwamnan wanda ya tattauna da gidan Talabijin na Channels ya zargi ‘yan siyasa da sabbaba rikicin masarautar sai dai ya bayyana fatan cewa za a warware komai nan bada jimawa ba.

Ya ce, “Ni babban dan majalisar masarautar ne, kuma baya ga haka na mulki jihar. Don haka ni babba ne a jihar. Daga ranar da batun yaje kotu na ce bazan yi magana ko shiga lamarin ba.

” Abin yana damuna. Ni dan Kano ne. Ina son komai ya zauna lafiya a Kano. Muna jira kuma ina fatan komai zai daidaita nan bada jimawa ba.

“Siyasa ce duk ta kai mu ga wannan rikici”, inji Shekarau.