Home Labarai El-Rufa’i ya naɗa sabon Sarkin Jere, shekaru 2 bayan rasuwar tsohon Sarkin

El-Rufa’i ya naɗa sabon Sarkin Jere, shekaru 2 bayan rasuwar tsohon Sarkin

0
El-Rufa’i ya naɗa sabon Sarkin Jere, shekaru 2 bayan rasuwar tsohon Sarkin

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya amince da naɗin Abdullahi Daniya a matsayin sabon Sarkin Jere.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa sabon Sarkin ya gaji Saad Usman ne, wanda ya rasu a ranar 1 ga watan Afrilu, 2020.

Naɗin Daniya ɗin na kunshe a wata takardar sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 9 ga watan Nuwamba, wacce gwamnan ya sanya wa hannu da kansa.

A wasiƙar, gwamnan ya ce nadin ya faru ne bisa ikon da dokar nadi da sauke Sarki ta 21 ta 2021 ta bashi a matsayin gwamna ya naɗa Daniya a matsayin Sarki mai daraja ta 2, a masarautar Jere, Ƙaramar Hukumar Kagarko.

Ya kuma yi kira ga Sabon Sarkin da ya sauke nauyin da ya hau kansa na yin mulki da adalci a matsayin sa na uban ƙasa, ba ma a masarautar sa ba kaɗai, ga ma ɗaukacin jihar Kaduna.

El-Rufa’i ya kuma yi masa addu’ar Allah Ya kama, inda ya ƙara da cewa nan gaba kaɗan za a yi bikin bashi sandar sarauta.