Home Labarai An rufe gidan marayu a Abuja bisa zargin safarar yara 23

An rufe gidan marayu a Abuja bisa zargin safarar yara 23

0
An rufe gidan marayu a Abuja bisa zargin safarar yara 23

Hukumar Babban Birnin Tarayya, FCTA, ta rufe gidan marayu na Priesthood Orphanage da ke kauyen Karon Majigi, Abuja, bayan kuɓutar da wasu yara 23 da ke tsakanin shekara daya zuwa 14 a gidan marayun, bayan zargin an yi safarar su daga jihar Plateau.

Adedayo Benjamins Laniyi, babbar sakatariyar hukumar FCTA, ita ce ta bayyana hakan yayin da take mika yaran ga kwamishiniyar mata ta jihar Plateau, Caroline Dafur, a Abuja a jiya Litinin.

Ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Misis Benjamins-Laniyi ta kuma ce, Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya baiwa sakatariyar izinin bincike tare da sake tantance gidajen marayu da ke aiki a cikin babban birnin kasar.

“Yin amfani da wannan a matsayin misali, daya daga cikin abubuwan da na fara yi shi ne na samu amincewar sake tantance gidajen marayu a Abuja.

“Ministan ya amince da cewa za a yi cikakken bayani da kuma sake tantance duk wani abu da ya shafi gidajen marayu a Abuja,” in ji ta.

Sakatariyar ta ce tuni Sakatariyar ta hada kai da Mrs Dafur domin sada yaran da iyalansu.

Ta kara da cewa wasu daga cikin yaran sun kasance a gidan marayun tun 2019.