Home Labarai Rukuni na 3 na ɗaliban da Kano ta ɗauki nauyin karatunsu sun tashi zuwa India

Rukuni na 3 na ɗaliban da Kano ta ɗauki nauyin karatunsu sun tashi zuwa India

0
Rukuni na 3 na ɗaliban da Kano ta ɗauki nauyin karatunsu sun tashi zuwa India

Rukuni na uku mai dalibai 159 ƴan asalin jihar Kano, daga cikin dalibai 1,001 da suka kammala karatun digiri na farko da gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin karatunsu zuwa kasashen waje, sun tashi zuwa kasar India domin yin karatun digiri na biyu a fannoni daban-daban.

Da yammacin ranar Juma’a ne daliban su ka tashi daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano, a kan idon kwamishinan ilimi mai zurfi, Dr Yusuf Kofarmata da sauran jami’an gwamnati domin yin bankwana da ɗaliban.

Da ya ke jawabi kai tsaye bayan tashin jirgin, Dr Kofarmata ya ce tashin rukunin na uku ci gaba ne a cikin alkawarin gwamnati na aiwatar da shirin bayar da tallafin karatu na digiri na biyu na shekarar 2023/2024.

Ya ce wadanda suka ci gajiyar tallafin, idan sun isa Indiya, za a kai su jami’o’in Indiya guda bakwai, da suka hada da Mewar, Sharda, Sri Sai, Swarnnim, SR, Symbiosis da Jami’ar Kalinga don yin karatun digiri na biyu.

Dr Kofarmata ya bayyana cewa daliban sun kammala karatun digiri na farko ne wadanda aka zabo su bisa cancanta da la’akari da kwazon da suka yi a matakin farko.

Kwamishinan ya yi bayanin cewa wadanda suka ci gajiyar shirin za su yi karatu ne a fannonin kwarewa na kasa da kasa domin cike gibin ma’aikata a jihar da ma kasa baki daya.

Ya kuma yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar bisa cika alkawarin da ya dauka lokacin yakin neman zabe na cewa zai dauki nauyin dalibai don su karo karatu a ƙasashen waje.